Aboki ya guntule ma abokinsa hannu bayan fada ya kaure a tsakaninsu saboda budurwa

Aboki ya guntule ma abokinsa hannu bayan fada ya kaure a tsakaninsu saboda budurwa

Rundunar Yansandan garin Zuba dake babban birnin tarayya Abuja ta kama wani matashi mai suna Yusuf Hassan inkiya Dakwa wanda ake zarginsa da sare ma abokinsa hannu mai suna Abubakar Umar, inji rahoton Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rikici ya kaure ne a tsakanin matasan akan wata budurwa da guda daga cikinsu ke so, inda a wannan rana na Dakwa ya bi Abubakar har gida, inda ya bukaci ya fito su dambace, fitowarsa keda wuya ya kai masa sara.

KU KARANTA: Magori wasa kanka da kanka: Na fi Buhari mutunci da kima a idon duniya – inji dan takarar shugaban kasa

Sai dai Abubakar ya bayyana cewa yarinyar da ake rikici akanta ta fito ne daga jihar Kaduna tare da mahaifiyarta inda suka zo garin Zuba don gudun hijira sai dai basu samu wajen zama ba, hakan ya say a basu dakinsa dake cikin gidansu, shi kuma ya koma ya tare a dakin abokinsa Dakwa.

Aboki ya guntule ma abokinsa hannu bayan fada ya kaure a tsakaninsu saboda budurwa
Yusuf

Ana cikin hakan haka ne sai Dakwa ya fara soyayya da yarinyar, amma bayan kwana biyu sai ya fara zargin wai Yusuf yana neman yarinyar shi ma, wannan dalilin da ya haifar da rashin jituwa a tsakaninsu, har ta kai ga amincin ya lalace kuma Dakwa ya fara yi ma Yusuf barazana.

Wadanda suke da masaniya game wannan tirka tirka sun tabbatar da cewar akwai lokacin da Dakwa ya kwaso wasu yan daba guda biyar da nufin su kassara Yusuf a yayin da yake gona tare da mahaifinsa, amma yan daban suka yi.

Har sai ranar da yazo gidansu Yusuf yana ta zage zage wai ya fito suyita ta kare, “Dana fito ne sai ya dauke adda ya kai mani sara a wuya, ni kuma na kare da hannuna, nan take hannun ya guntule, shi kuma a yayi kokarin tserewa, amma matasan unguwa suka kama shi.” Inji Yusuf.

Kaakakin Yansandan yankin, CSP Fodiyo Sani ya tabbatar da faruwar lamatin, inda yace zasu gurfanar dasu gaban Kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel