Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kashe wasu gungun 'yan ta'adda a jihar Zamfara
Rundunar sojin saman Najeriya wacce ake yiwa inkiya da 'Operation Diran Mikiya' ta bayyana cewa sun samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda masu yawan gaske a dajin Sububu
Rundunar sojin saman Najeriya wacce ake yiwa inkiya da 'Operation Diran Mikiya' ta bayyana cewa sun samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda masu yawan gaske a dajin Sububu, Birnin Magaji da kuma dajin Rugu dake cikin jihar Zamfara. Harin wanda suka gabatar da shi ta hanyar amfani da jiragen yaki na sama, sun kai shine a ranekun 9 zuwa 11 na wannan watan.
DUBA WANNAN: Likitoci zasu tafi yajin aiki a Abuja
A wata sanarwa da kakakin rundunar ya fitar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce harin da suka kai dajin Sububu, sun kai shine a ranar 9 ga wannan watan, bayan sun gano wani sansani na 'yan ta'addar a dajin.
Ya kara da cewa rundunar tasu ta kara kai wani sabon hari akan sansanin wasu 'yan ta'adda a kauyen Galadi dake yankin arewa maso yammacin jihar ta Zamfara.
"Rundunar mu ta tashi jirgin yaki dauke da dakaru inda suka nufi dajin Sububu, ba a jima ba suka hango sansanin 'yan ta'addar, inda ba makawa suka hau su da harbi suka tarwatsa su," inji Daramola.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng