Zaben 2019: Ina goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari - Sanata Danjuma Goje

Zaben 2019: Ina goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari - Sanata Danjuma Goje

Mun ji labari cewa wani Sanata na Jam’iyyar APC mai mulki ya karfafa yakin neman zaben Shugaba Buhari. Wani fitaccen Sanata ne daga Arewa yayi alkawarin marawa Shugaba Buhari baya.

Zaben 2019: Ina goyon bayan tazarcen Shugaba Buhari - Sanata Danjuma Goje

Sanata Goje yace ba zai bi sahun su Saraki da Kwankwaso ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kwarin gwiwar fitowa takarar 2019 da kyau inda Sanata Muhammad Danjuma Goje ya bayyana cewa zai yi bakin kokarin sa wajen ganin Shugaban kasar ya koma kan kujerar sa a badi.

Sanatan na APC Danjuma Goje ya tabbatar da mubaya’ar sag a Jam’iyyar APC mai mulkin kasar ya kuma jaddada shirin sa na ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin nasara a zabe mai zuwa na 2019 wanda yake daf da kunno kai.

KU KARANTA: Jerin wasu manyan ayyuka na Gwamnatin Buhari

Sanata Goje ya bayyana wannan ne jiya ta shafin sa na Tuwita da sassafe wanda har ya jawo wasu ‘Yan Majalisu su ka fara tofa albarkacin bakin su. Wani ‘Dan Majalisar Kano yayi alkawarin tona asirin Sanatan bayan yayi wannan jawabi.

Dama dai kun ji labari cewa duk da sauya shekar da wasu Sanatoci su ka yi, Jam’iyyar APC na cigaba da kara yawa a Majalisa bayan zabukan da aka yi jiya. APC ake tunani za ta lashe zaben kujerar Sanatan Kudancin Bauchi da Arewacin Katsina.

Dazu kun ji labari cewa INEC ta fitar da sakamakon zaben Sanatan Yankin Daura a Jihar Katsina na akwatin Unguwar Sarkin Yara ‘A’ wanda nan ne inda Buhari yake zabe. APC ta samu kuri’a 1984 yayin da PDP kuma ta tashi da kuri’u 255 rak.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel