Daruruwa ne suka mutu a ambaliyar ruwan da aka tafka a Indiya

Daruruwa ne suka mutu a ambaliyar ruwan da aka tafka a Indiya

- Ambaliya na aruwa ne saboda dumamar yanayi

- Indiya kasa ce ta biyu a yawan jama'a, wadanda mafi yawansu a kauyuka suke

- Ruwan ya kashe mutum 500

Daruruwa ne suka mutu a ambaliyar ruwan da aka tafka a Indiya
Daruruwa ne suka mutu a ambaliyar ruwan da aka tafka a Indiya

Ruwan sama da aka shafe kwanaki ana tafka shi a kasar Indiya, ya kashe akalla mutane 500 a wani bala'i da aka dade ba'a ga irin sa ba a fadin kasar nan.

Ruwan ya kuma share unguwanni da gidaje, inda kuma ya kori akalla mutum 100,000 daga muhalansu a fadin kasar.

DUBA WANNAN: Sabbin hanyoyin shigo da man fetur arewa

Yanzu haka gwamnati na shiirin kai agajin gaggawa ga jama'a inda kuma masoya suka bazama neman yan'uwansu, da rai ko babu.

Dumamar yanayi ce ummul-aba-isin da yasa ake sake ganin ambaliya mai karfi irin wannan a sassan duniya, inda iska mai dumi tafi daukar danshi da ke zama hadari ya saki ruwan sama, bayan rana ta dumama teku.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel