Mafarauta sun nemi izinin mamaye dajin Sambisa don farauto Shekau da rai ko babu rai

Mafarauta sun nemi izinin mamaye dajin Sambisa don farauto Shekau da rai ko babu rai

Dubunan mafarauta ne suka bayyana cewar tsaf zasu iya fadawa dajin Sambisa kuma har su farauto shugaban kungiyar yan ta’addan Boko Haram, Abubakar Shekau a duk inda yake, ko da rai ko babu rai, inji rahoton jaridar The Cables.

Wani daga cikin manyan shuwagabannin kungiyar mafarautan, Bukar Mustapha ne ya bayyana mamajiyar Legit.ng haka, inda yace akwai sama da mafarauta dubu ashirin da suka shirya don afkawa Sambisa da wasu sassan yankin tekun Chadi don gamawa da yan Boko Haram.

KU KARANTA: Aiki ga mai kareka: Babban sufetan Yansanda ye nemi izinin yin binciken kwakwaf akan Lawal Daura

Sa’annan Bukar yace sun san dajin Sambida kamar ba gobe, duk wani lungu da sako na dajin sun san shi a yayin farauta da suke kwashe sama da shekaru Talatin suna yi: “Muna da irin nasu asirin da zai iya aika bala’I sansanin yan Boko Haram, wannan mun gaje shi ne a hannun iyaye da kakanni.” Inji shi.

Mafarauta sun nemi izinin mamaye dajin Sambisa don farauto Shekau da rai ko babu rai
Mafarauta

Bukar ya cigaba da cewa: “Kaga zamu iya tsayar da dajin cak! Komai ya tsaya inda yake, hakan zai bamu damar kama shekaua kamar zomo, mafarautanmu suna nan a dukkanin kananan hukumomi 27 na jihar, kuma mun shirya tsaf.

“Abinda muke nema daga Sojoji shine baburan, mun san duk inda Boko Haram ke boyewa, amma ba a bamu umarnin kamosu bane, ina ganin ya kamata Sojoi su fara daukan wasu daga cikinmu idan zasu shiga dajin Sambia, don mu nuna musu inda yan ta’addan suke boyewa.” Inji shi.

Daga karshe Bukar yace wannan yaki da ta’addanci ba yake bane kawai na Sojoji, ya kamata Musulmai, Kiristoci, Manoma, yan kasuwa da sauran kungiyoyin addinai da zasu taimaka ma Sojojin Najeriya a wannan muhimmin aiki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng