Babu mai tatsar Talakka kamar ma'aikatan sabuwar NEPA a jihohi - Kwastomomi
- Ana karawa kwastomomi kudin wuta sama da Naira tiriliyan 2 a duk shekara
- Kudin ya isa a gyara yanayin wutar kasar nan
- A kananan hukumomin kudu, suna tara kusan Naira miliyan 28 duk shekara ga kwastomo
Wasu masu amfani da wutar lantarki a karkashin Association for Public Policy Analysis sun ce kamfanoni 11 masu raba wutar lantarki na tara sama da Naira tiriliyan 2 a duk shekara ta hanyar bawa kwastomomi ba sahihin bill ba wanda wai ya isa a gyara tsarin wutar lantarki.
A wata maqaala ta shugaban APPA, Comrade Princewill Okorie, a ranar Alhamis yace hakan maida martani ne ga kamfanonin raba wutar lantarki da suka ce suna faduwa tun da masana'antar ta koma ta kudi.
Yace "Ana zargin cewa kamfanonin dake raba wutar lantarki suna samu sama da Naira tiriliyan 2 a duk shekara daga kwastomomi a karkashin kananan hukumomi 774 fadin kasar nan".
DUBA WANNAN: Saudiyya ta kirkiro manhajar tantance wa'azi
"Duk da haka sunce kudin su basu kaiwa tunda sunki su fitar da hanyar nuna shaidar kudin da suke shiga" inji APPA
Kungiyar tace a wani bincike da tayi, ta gano cewa a kananan hukumomi 95 na kudu maso yamman kasar na, suna samun kusan Naira biliyan 28 a duk shekara daga kwastomomi da ake karawa kudi daga kowacce karamar hukuma.
"A misali duk wata karamar hukumar jihar Imo, ana basu bill din Naira 750,000 a duk wata kuma basu samun wuta da ta kai ta kwanaki 15 a wata" kamar yanda binciken ya nuna.
APPA ta goyi bayan kiran da ministan wuta, aiyuka da gidaje yayi da a kara inganta yalwatar wutar lantarki balle kuma ta hanyar kawo karshen karin kudin ba bisa ka'ida ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng