Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane

Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane

- Zimbabwe ta shiga tsaka mai wuya saboda takunkumai

- Kudinsu sai a wheelbaro aje kwasar su

- An kori Mugabe daga mulki abubuwa sun fara gyaruwa

Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane
Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane

Kudi mafi daraja a duniya shine DInari na Kuwaiti, wanda yake da karfi kusan kwatankwacin gwal watau zinare, to ko kunsan kuma kudi mafi zama yayi da rashin albarka ko daraja a duniyarmu a yau?

Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane
Takardar kudi da sai an cika gingimari da ita zasu isa cefane

Wannan kudi shine na kasar Zimbabwe, wanda kafin a kansille shi kwata kwata a daina aiki dashi, sai da zairukansa suka doshi layi biyu.

Kudin dai, wanda ake kira dalar Zimbabwe, wanda ya rasa darajarsa, inda ko shebur guda aka ajje basu saya wa iyali biredi, ya rasa albarka ne bayan da turai suka sanya wa Mugabe tsohon shugaban da kasarsa takunkumai, saboda korar turawa da yayi a shekarun baya.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta kirkiro manhajar tantance wa'azi

Shi dai Mugabe, yace Afirka ta baqaqee ce, don haka babu yadda za'a yi ace Turawa sun gaji gonaki tafka tafka sun kuma dauki bakaken fata aikin leburanci a ciki.

An daina amani da kudin don ya zamo yayi inda aknga manyan motoci na yawo dashi don neman cefane ko kalaci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel