Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Za ku ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya tsige wasu kwamishinonin sa biyu da suka tarbi Sanata Godswill Akpabio tare da lale maraba yayin da ya sauka a filin jirgin sama dake babban birnin jihar na Uyo.

Kwamishinonin da suka debo ruwan dafa kansu sun hadar da; Victor Anatai na ma'aikatar al'adu da yawan buda idanu da kuma Ibanga Akpabio, na ma'aikatar kwadago wanda ya kasance dan uwa ga sanatan.

Sanata Akpabio wanda a ranar Talatar da ta gabata ya yi murabus daga kujerar sa ta shugaba na majalisar dattawa marar rinjaye, ya kada wata sabuwar guguwar siyasa a jihar Akwa Ibom yayin da yunkurin sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa ta jam'iyya mai ci ta APC.

Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Gwamna Emmanuel ya tsige Kwamishinonin sa 2 da suka yi lale maraba ta Sanata Akpabio

Bayan ganarwar sa da shugabannin APC na jihar da kuma kai ziyara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake hutun kwanaki 10 a birnin Landan, Sanata Akpabio ya kuma yada zango a jihar sa a ranar Talatar da gabata inda Mista Antai da kuma Mista Ibanga suka tarbe sa tare da wasu jiga-jigan 'yan siyasa.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan tarba tare da lale marhabun da kwamishinonin suka yiwa Sanatan ta janyo suka rasa aikin su kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya bayyana.

KARANTA KUMA: Biyayya ta ga Kwankwaso ya janyo ma ni cin kashi a jihar Kano - Hafiz Abubakar

Rahotanni sun bayyana cewa, Sakataren gwamnatin jihar, Emmanuel Ekuwem, shine ya bayar da sanarwar tsige kwamishinonin biyu sakamakon sabawa tsare-tsaren gwamnatin jihar.

Kazalika an umarce su akan mika ragamar aiki a hannun sakatarorin dindindin na ma'aikatun sa a ranar yau ta Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel