Buhari ne ya bayar da umarnin tsige Daura bayan gano wata kitimurmura tsakaninsa da Saraki

Buhari ne ya bayar da umarnin tsige Daura bayan gano wata kitimurmura tsakaninsa da Saraki

Sahara Reporters ta wallafa wani labara dake bayyana cewar saida mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya samu sahalewar Buhari kafin ya salami shugaban hukumar DSS, Lawan Daura, daga aiki.

Jaridar ta wallafa cewar tun da misalign karfe 4:00 na safiyar ranar Talata osinbajo ya samu amincewar Buhari a kan sallamar Daura daga aiki.

A cewar Sahara, shugaba Buhari ya gano cewar Daura da Bukola na aiki tare domin bata sunan gwamnatinsa a gida Najeriya da ma duniya baki daya.

Majiyar Sahara ta shaida mata cewar hatta mamaye harabar ginin majalisa da jami’an hukumar DSS suka yi, wani yunkuri ne da Daura ya yi domin nemawa Saraki suna ta hanyar nuna gwamnati na muzguna masa saboda ya fita daga jam’iyyar APC.

Buhari ne ya bayar da umarnin tsige Daura bayan gano wata kitimurmura tsakaninsa da Saraki

Lawal Daura

Tuni fadar shugaban kasa ta bayyana cewar babu hannun shugaba Buhari ko na mataimakinsa a yunkurin jami’an tsaron hukumar DSS hana shiga ginin majalisar a yau, Talata.

DUBA WANNAN: An kama Lawal Daura an tsare bayan Osinbajo ya kore shi daga aiki

Labarin da jaridar Legit.ng ta samu ya tabbatar mata da cewar hadakar jami’an tsaron hukumar ‘yan sanda da na SARS sun kama shugaban hukumar tsaro ta DSS, Lawal Daura, da Osinbajo ya sallama daga aiki yau dinnnan.

An kama Daura ne bisa zarginsa da katsalandan a zaman lafiyar kasa. Yanzu haka yana tsare a shelkwatar SARS ta kasa bisa zarginsa da tayar da zaune tsaye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel