Zan hukunta duk wadanda suka shirya ma Majalisa manakisa – Inji Mukaddashin shugaban kasa
Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana tare ma yan majalisun dokokin Najeriya tare da hanasu shiga wajen aikinsu a matsayin abin kunya, kuma abin Allah wadai, kuma cin mutuncin kundin tsarin mulkin Najeriya ne.
Legit.ng ta ruwaito Kaakakin Osinbao, Laolu Akande ya bayyana cewa mukaddashin shugaban bai ji dadin matakin da hukumar DSS ta dauka ba akan majalisa ta hanyar tura jami’anta suka hana Sanatoci shiga majalisa, kuma yace ba da izininsa DSS suka aikata hakan ba.
KU KARANTA: Yanzu yanzu: Mukaddashin shugaban kasa ya tsige shugaban hukumar DSS
Sai dai tuni da Farfesa Osinbajo ya sallami shugaban hukumar DSS, Lawal Daura daga aiki, sa’annan ya bada umarnin garkameshi har sai abinda hali ya yi, haka zalika Osinbajo ya dauki alwashin hukunta duk masu hannu cikin shirya wannan manakisa.
Idan za’a tuna, da safiyar yau ne jami’an DSS suka tare kofar shiga majalisar dokokin Najeriya, inda suka hana wasu Sanatocin jam’iyyar PDP shiga farfajiyar majalisar, duk da cewa majalisar na hutu, har sai watan Satumba za’a bude ta.
Sai daga daga bisani bayan yan majalisun sun matsa, jami’an sun bude musu hanya, wannan tataburza da aka sha tsakanin Sanatoci da Jami’an DSS ya biyo bayan jita jitan da ake yadawa na cewa wai Sanatocin APC zasu tsige shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng