2019: An sami ragin farashin tikitin takarar shugaban kasa a PDP mai adawa daga N20m

2019: An sami ragin farashin tikitin takarar shugaban kasa a PDP mai adawa daga N20m

Babbar jam'iyyar hamayyar ta kalubalanci Buhari da kulle kullen tsige Bukola Saraki da Ekweremadu da karfin tsiya. Ta kuma zargi shugaban kasa da muna munar yanda zasu lashe zaben 2019, cewa da suna tsoron faduwa warwas.

2019: An sami ragin farashin tikitin takarar shugaban kasa a PDP mai adawa daga N20m
2019: An sami ragin farashin tikitin takarar shugaban kasa a PDP mai adawa daga N20m

Jam'iyyar PDP ta yanke Naira miliyan 12 a matsayin kudin siyan tikitin neman shugabancin kasa a karkashin inuwar ta.

Jam'iyyar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC da laifin bata musu suna domin suna tsoron faduwa zaben 2019.

Ta kara da cewa shugaban yana son tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da mataimakin shi, Sanata Ike Ekweremadu da karfin tsiya.

Kamar yanda jadawalin su na siyar da tikitin ya nuna na zaben fitar da gwani, wanda majiyar mu ta gani a ranar litinin, nuna ra'ayin siyan tikitin shugabancin kasar Naira miliyan 2 ne, shi kuma tikitin Naira miliyan 10 ne.

Tikitin takarar gwamnoni a karkashin inuwar jam'iyyar kuwa Naira miliyan 6 ne, na sanatoci kuma Naira miliyan 3.5 ne.

A hakan kuma jam'iyyar tace tikitin takarar majalisar wakilai Naira miliyan 2.5 ne, sai kuma na majalisar jiha Naira dubu dari shida ne.

Kamar yanda INEC ta sanar, zaben fitar da gwani na shugabancin kasa, gwamnoni, majalisar tarayya da ta jiha zai fara ne a 18 ga watan Augusta, ya kare a watan Octoba na 2018. Shi kuma na yankin birnin tarayya zai fara ne a 4 ga watan Satumba, ya kare a 27 ga watan Octoba na 2018.

DUBA WANNAN: In sun kawo ku amsa, amma ku kada su

Babbar jam'iyyar hamayyar ta kalubalanci Buhari da kulle kullen tsige Bukola Saraki da Ekweremadu da karfin tsiya. Ta kuma zargi shugaban kasa da muna munar yanda zasu lashe zaben 2019, cewa da suna tsoron faduwa warwas.

Jam'iyyar ta kalubalanci shugaban akan waskar da Naira tiriliyan 9 na kudin danyen man fetur. Sannan kuma ta bukaci shugaban da ya fadi dalilin da ya hana shi binciko jami'an mulkin shi wadanda aka kama da laifin rashawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel