Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa

Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa

Wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ci karo das hi ya tabbatar da cewar an saki Sheikh Ahmad al-Garkawi, fitaccen malamin addinin Islama da wasu ‘yan bindiga suka sace tare da wasu dalibansa ranar Alhamis a Kaduna.

An saki makamin ne bayan biyan kudin fansa, miliyan N10m, kamar yadda majiyar mu ta tabbatar.

A ranar Alhamis ne wasu yan bindiga da suka yi awon gaba da fitaccen Malamin addinin Musunluncin nan dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Al-Garkawy tare da wasu dalibansa.

Jaridar Desert Herald ce ta ruwaito wannan labari, inda tace yan bindigan sun yi garkuwa da shehin Malamin tare da dalibansa ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Agusta, a daidai lokacin da suka kai ziyara gonar makarantarsa dake gefen garin Kaduna.

Masu garkuwa sun saki Sheikh Al-Garkawy bayan karbar miliyoyin kudin fansa
Sheikh Al-Garkawy

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar zuwa yanzu har ‘yan bindigar sun nemi iyalan Malamin dasu biya kudin fansa kafin su sake shi tare da daliban nasa, sai dai ba’a bayyana adadin kudin da suka nema ba.

A yanzu haka hankulan jama’an unguwar da Malamin ke zaune, Unguwar Mu’azu dake cikin garin Kaduna ya tashi matuka, sakamakon suna amfana kwarai da gaske da Malam, ta karatuttukan da yake yi a kullum, da kuma makarantu da asibitocin da yake assasawa.

DUBA WANNAN: Bambarakwai: 'Yan shi'a sun yi mauludin annabi Isa a Kaduna, hotuna

Duk da irin kokarin da gwamnatin tarayya take yi game da yaki da masu garkuwa da mutane a Najeriya, amma ayyukansu na cigaba da ta’azzara a yankin Arewa maso yamma, musamman ma a jihar Kaduna, lamarin da yafi shafar al’ummar garin Birnin Gwari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel