Sanata, tsohon minista da wasu 13 sun canja sheka daga PDP zuwa APC
Sanata mai wakiltar jihar Ebonyi ta kudu a majalisar dattijai, Sonni Ogbuoji, da tsohon karamin ministan tama da karafa, Goddy Ogbaga, da wasu mutane 13 sun canja sheka zuwa APC daga PDP a jiya, Asabar.
Masu canja shekar sun sanar da komawar su jam'iyyar APC ne yayin wani taron gangamin jam'iyyar da aka shirya a jihar Ebonyi domin karrama Adams Oshiomhole da shugaba Buhari.
Da yake jawabi ga masu canjin shekar, Oshiomhole ya jinjinawa Ogbuoji da ragowar mutanen bisa karfin halin da suka nuna na barin PDP tare da shiga APC. Ya kara da cewar gwamnatin tarayya na matukar kokari wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasar nan.
"Yanzu muna da zababben sanata, Cif Sonni Ogbuoji, da ya fita daga inuwar laimar PPD da ta dade da lalacewa," a cewar Oshiomhole.
Sannan ya kara da cewa, "ya shigo jam'iyyar APC ne bayan gamsuwa da irin salon mulkin shugaba Buhari a karkashin jam'iyyar da kuma ganin yadda batagari suka shiga jam'iyyar PDP."
DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP da ya koma APC ya gana da Buhari a Ingila
A nasa jawabin, ministan kimiyya da fasaha, Dakta Obonnaya Onu, ya bayyana cewar tuni mutanen jihar Ebonyi suka yanke shawarar hada gwuiwa da jam'iyyar APC domin sake zaben shugaba Buhari a 2019.
Kazalika ya bukaci dukkan jihohin yankin kudu maso gabas da suka hada da, Abia, Imo, Ebonyi, Anambra da Enugu da su rungumi jam'iyyar APC domin cigaban yankin da ma Najeriya baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng