Da duminsa: Tsohon gwamnan PDP da ya koma APC sun gana da Buhari a Ingila, duba hotuna

Da duminsa: Tsohon gwamnan PDP da ya koma APC sun gana da Buhari a Ingila, duba hotuna

An yi wata ganawa tsakanin shugaba Muhammadu Buhari dsa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, a kasar Ingila.

Idan baku manta ba, a jiya, Asabar, ne mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dattijai, Ita Enang, ya tabbatar da cewar Akpabio ya canja sheka daga PDP zuwa APC har ya sanar da cewar za a yi bikin karbar sa ranar 8 ga watan Agusta da muke ciki.

Tsohon gwamna Akpabio na daga kusoshin jam'iyyar PDP a yankin kudu maso kudu mai arzikin man fetur.

Akwai rahotannin cewar wasu gwamnoni PDP daga kudancin Najeriya zasu koma APC kafin zaben 2019.

Da duminsa: Tsohon gwamnan PDP da ya koma APC sun gana da Buhari a Ingila, duba hotuna

Buhari da Akpabio a Ingila

Da duminsa: Tsohon gwamnan PDP da ya koma APC sun gana da Buhari a Ingila, duba hotuna

Akpabio da Buhari

Enang ya sanar da hakan ne a jiya, Asabar, a shafinsa na Tuwita tare da bayyana cewar za a yi bikin karbarsa ranar 8 ga watan Agusta a jiharsa ta Akwa Ibom.

DUBA WANNAN: Mabiya Shi'a sun yi mauludin annabi Isa a Kaduna, duba hotuna

Ina mai tabbatar da tabbatarwa da jam’iyyar APC cewar, kamar yadda muka bayyana a baya, za a karbi Godswill Akpabio zuwa APC a ranar 8 ga watan Agusta a jihar Akwa Ibom”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

An dade ana jitar-jitar cewar tsohon gwamnan zai koma jam’iyyar APC musamman ganin yadda ya cigaba da kauracewa taron jam’iyyar PDP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel