Kotu ta sanya ranar da zata sako Zakzaky
A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar kotu a jihar Kaduna ta sanya 4 ga watan Oktobar nan ya zamo ranar da zata zauna akan bukatar belin shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi wato Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matar shi Zinat
A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar kotu a jihar Kaduna ta sanya 4 ga watan Oktobar nan ya zamo ranar da zata zauna akan bukatar belin shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi wato Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky da matar shi Zinat.
Alkalin mai shari'a, Gideon Kurada, ya dage sauraron shari'ar bayan da Mista Maxwell Kyon, lauyan Zakzakyn ya bukaci a bada belin shi.
DUBA WANNAN: El-Rufai ya tunbuke wani Sarkin gargajiya a jihar Kaduna
Kyon yace masu kare shugaban sun bukaci belin shi ne, kuma wadanda suke karar ma sun maida martanin su.
Yace 4 ga watan Octoba ne za a zauna akan zancen belin.
Lauyan masu kara, Chris Umar, ya tabbatar wa da ofishin dillancin labarai, bayan zaman kotun cewa an isar wa da lauyoyin wanda ake kara na 3 da na 4 ta wani rubutu a jaridun Daily Trust da The Nation.
Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta kawo laifuka 8 da ake tuhumar Zakzakyn dasu, matar shi da wasu shugabannin kungiyar guda biyu da suke zama a katsina da kano.
Sheikh Zakzaky, matarshi, Yahaya da Abdulqadir duk an kaisu kotu ne da zargin hadin kai gurin tada zaune tsaye da kuma taimakawa gurin kashe kashe da dai sauran laifuka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng