Zazzabin wata zai haifar da matsanancin duhu a Najeriya ranar juma’a – Masana kimiyya

Zazzabin wata zai haifar da matsanancin duhu a Najeriya ranar juma’a – Masana kimiyya

A daren gobe, Juma’a, ne ake zaton samun nusanin wata da ba a taba fuskantar irinsa ba a tarihin Najeriya, kamar yadda Farfesa Augustine Ubachukwu, na bangaren ilimi da binciken sanin sararin samaniya a jami’ar Najeriya dake Nsukka ya sanar.

Farfesa Ubachwukwu, wanda ya kasance shugaban sashen bincike da ilimin sanin sararin samaniya, ya sanar da hakan ne yau, Alhamis, a Abuja yayin wata ganawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).

“Najeriya zata fuskanci zazzabin wata a ranar juma’a, 27 ga watan Yuli. Za a samu daukewar hasken farin wata daga karfe 9:30 na dare har zuwa karfe 11:22,” a cewar Farfesa Ubachukwu.

Zazzabin wata zai haifar da matsanancin duhu a Najeriya ranar juma’a – Masana kimiyya
Zazzabin wata

Farfesa ubachukwu ya kara da cewar wannan shine zazzabin wata mafi tsawo da za a gani a karon farko tun bayan wasu shekaru daruruwa da suka wuce kuma zai shafi sassann duniya da suka hada da Turai, Afrika, Asia, Australia da New Zealand.

A cewar Farfesa Ubachukwu, zazzabin wata ba kamar na rana ne, a saboda haka jama’a kan iya ganinsa da idonsu ba tare da amfani da gilashin kare idanu ba.

DUBA WANNAN: Kotun kasar Amurka tayi watsi da karar da Biyafra ta shigar da gwamnatin Najeriya

Masanin ya bayyana cewar bayan wannan zazzabin watan, Najeriya zata kara fuskantar irinsa a watan Janairu na shekarar 2019.

Wani masanin ilimin sararin samaniya, Farfesa Rabi’u Babatunde, na cibiyar binciken sararin samaniya dake jihar Kogi ya bukaci jama’a da kada su damu da zazzabin da watan zai yi domin hakan na daga cikin shaidar cewar duniyar mu ba a tsaye take wuri guda ba, wato tana motsi ko a ce juyawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel