Mun yi sak a 2015 amma a zaben 2019 kila ‘Dan ba-kara – Inji wani babban Masoyin Buhari

Mun yi sak a 2015 amma a zaben 2019 kila ‘Dan ba-kara – Inji wani babban Masoyin Buhari

Labari ya zo mana cewa wani Bawan Allah wanda yana cikin manyan Magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi tir da Gwamnatin nan ta APC inda yace idan ta kama a kore sa daga Jam’iyyar APC mai mulki to ta fi nono fari.

Mun yi sak a 2015 amma a zaben 2019 kila ‘Dan ba-kara – Inji wani babban Masoyin Buhari
Wani Masoyin Buhari yace idan abubuwa ba su gyaru ba za ta sake zani

Dr. Nura Alkali wanda da su aka fara tafiyar Shugaba Buhari tun tale-tale ya nuna rashin jin dadin sa da wannan Gwamnati a wani dogon bayani da yayi a shafin sa na Facebook. Alkali yace kila shi da Iyalin sa duk ba za su yi APC ba a 2019.

Nura Alkali wanda babban Likita ne da ake ji da shi ya bayyana cewa Iyalin sa sun a kokawa da tsadar kayan masarufi a Gwamnatin Buhari. Bayan nan kuma yake cewa ‘Ya ‘yan sa da sauran mutanen sa su na kuka da mulkin APC.

KU KARANTA: Mun bani mun lalace idan Buhari ya zarce inji Fayose

Babban Masanin ya nuna cewa zai dai yi wahala APC ta iya samun nasarar da tayi a 2015 a zabe mai zuwa. Don haka ne ma yace Jam’iyyar mai mulki na iya shan kashi a zaben 2023 lokacin da Shugaba Buhari ya kammala wa’adin sa.

Wasu matakan da Buhari ya dauka kamar na yin shiru game da zargin da ke kan wuyar Minista Kemi Adeosun na amfani da takardun shaida na bogi ya fusatar da Nura Alkali wanda yace idan ba a gyara ba sun raba Jiha da Buhari a 2019.

Dr. Nura Alkali yace idan har Shugaban Kasa Buhari bai shawo matsalar harkar tsaro da matsin tattalin da ake fama da shi ba to babu mamaki kaf Iyalan sa ba za su zabe sa ba. Dazu kuma kun ji yadda Sanata Shehu Sani ya soki Gwamnatin Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng