An kulla sharudan yin aiki tare tsakanin Shekarau da Kwankwaso a PDP
Tun kafin dawowar Kwankwaso jam’iyyar PDP ake ta bayyana mabanbantan ra’ayi a kan yadda zasu yi aiki tare tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Kano, Shekarau, dake rike da PDP bayan ficewar Kwankwaso.
Yanzu dai bayanai a kan yadda tsofin gwamnonin biyu zasu yi aiki tare sun fito, kamar yadda wani rahoton jaridar Today Nigeria ya wallafa.
Abu na farko daga cikin sharudan da tsofin gwamnonin suka cimma kuma zasu mayar da hankali kai shine batun kayar da gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zaben shekarar 2019.
Jaridar ta bayyana cewar wata majiya ta sanar da ita cewar Shekarau ya amince zai mika ragamar jam’iyyar PDP a jihar Kano ga Kwankwaso muddin ya fita daga jam’iyyar APC. Majiyar ta bayyana cewar Shekarau ya amince da yin hakan ne saboda sanin sirrin gwamna Ganduje da ya yi.
Domin samun dammar kayar da Ganduje cikin sauki, Shekarau ya bar wa kwankwaso zabin fitar da dan takarar gwamna shi kuma ya bayar da mataimaki. Majiyar jaridar ta sanar da ita cewar Kwankwaso na shirin tsayar da mataimakin gwamna Ganduje, Farfesa Hafiz Abubakar, a matsayin dan takarar gwamna a PDP.
DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan majalisar dokokin jihar Kano 6 da zasu bi Kwankwaso PDP
Ana saka ran Farfesa Hafiz zai sanar da komawarsa jam’iyyar PDP kowanne lokaci daga yanzu.
Tun a shekarar 2017 ne ta bayyana a fili cewar akwai Baraka tsakanin gwamna Ganduje da mataimakinsa, Farfesa Hafiz.
Tuni Farfesa Hafiz ya bayyana aniyarsa ta komawa jami’a a shekarar 2019 domin cigaba da aikinsa na koyarwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng