Da dumi dumi: Sarkin Katsina ya nada sabon Sardaunan Katsina bayan mutuwar Coommassie
A ranar Litnin, 23 ga watan Yuli ne masarautar Katsina ta sanar da amincewan Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman da nadin Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Sardaunan Katsina, inji rahoton Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sallaman Katsina, sakataren majalisar Sarki, Alhaji Bello Ifo ne ya sanar da haka, inda yace an nada Ida ne bayan mutuwar tsohon sardaunan Katsina Ibrahim Coommassie wanda ya rasu a Alhamis din data gabata.
KU KARANTA: Kifa daya kwala: Wani matashi ya yi ma abokinsa duka daya har lahira akan N100
Kafin nadinsa, Ibrahim Ida ne Dan majen Katsina, kuma an haifeshi a ranat 15 ga watan Janairu na shekarar 1949 a jihar Katsina, sa’annan yayi katarunsa a jami’ar Ibadan da jami’ar Abuja, daga bisani ya zama kwamishinan kudi a jihar Katsina.
Bayan fadarwarsa fagen siyasa aka zabe shi a Sanatan mai wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar dattawa a shekarar 2007 a karkashin jam’iyyar PDP, inda a yanzu ya sauya sheka zuwa APC.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng