'Yan takarar Kujerar Gwamna 8 na jam'iyyar PDP za su gudanar da yarjejeniya a jihar Kaduna

'Yan takarar Kujerar Gwamna 8 na jam'iyyar PDP za su gudanar da yarjejeniya a jihar Kaduna

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, kimanin 'yan takara 8 na kujerar gwamnatin jihar Kaduna karkashin lema ta jam'iyyar PDP, sun shirya tsaf tare da amincewa da gudanar da yarjeniyar tsayar dan takara daya a zaben 2019.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne daya daga cikin manema takarar, Dakta Ja'afaru Sa'ad, ya bayyana hakan a birnin Kaduna da cewar wannan kyakkyawan yunkiri ne da ya cancanci yabo.

Sa'ad wanda ke rike da sarautar Galadiman Ruwan Zazzau ya bayyana cewa, manufar wannan shawara ita ce baiwa jam'iyyar PDP dama ta karfafuwa domin lallasa duk wani tankara da jam'iyyar APC za ta tsayar a zaben 2019.

Yake cewa, wannan yunkuri zai baiwa jam'iyyar damar daura damarar da daukan sulke da makaran garkuwa domin fafata yakin kwatar mulki daga hannun jam'iyyar APC.

'Yan takarar Kujerar Gwamna 8 na jam'iyyar PDP za su gudanar da yarjejeniya a jihar Kaduna
'Yan takarar Kujerar Gwamna 8 na jam'iyyar PDP za su gudanar da yarjejeniya a jihar Kaduna
Asali: Depositphotos

Sauran manema takara da suka shirye hade kai sun hadar da; Malam Isah Ashiru, Muhammad Sani Bello, Bello Kagarko, Sani Sidi, Jonathan Kish, Shu'aibu Mikati da kuma tsohon gwamnan jihar, Alhaji Ramalan Yero.

Legit.ng ta fahimci cewa, babbar manufar wannan yarjejeniya ta 'yan takarar itace lallasa duk wani dan takara da jam'iyyar APC za ta tsayar a zaben 2019 mai gabatowa.

KARANTA KUMA: Hukumar Kastam reshen Apapa ta samar da N176.7bn na kudaden shiga cikin watanni shida

A yayin tabbatar da wannan lamari, Malam Ibrahim Wusuno, sakataren jam'iyyar na jihar, ya bayyana cewa wannan shawara yarjejeniya ce ta dattawa, mambobi da jiga-jigan jam'iyyar.

Kazalika, Sa'ad ya nemi rassan jam'iyyar dake sauran jihohin kasar nan kan daukar wannan mataki a mukaman kujeru daban-daban da kuma kujerar shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel