Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa

Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa

Masana sana’ar nishadantarwa sun yi ittifakin masana’antar shirya shirya fina finan Hausa dake da shelkwata a jihar Kano, wanda aka fi saninta da suna Kannywood na daya daga cikin masana’antun fim na Duniya dake samun cigaba.

Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna wannan cigaba da na nasaba da al’adar Hausa dake da armashi, wanda shine yaren da ake gudanar da wadannan fina finai dasu, inda a yanzu haka Kannywood na daya daga cikin manyan masana’antun dake baiwa matasan Arewa aikin yi.

Majiyar Legit.ng ta kawo wasu jaruman dake taka a wannan masana’anta maza da mata da taurauwarsa ke haskawa fiye da na sauran, daga cikinsu akwai;

KU KARANTA: Ambaliyar Katsina: Yadda ya ruwa ya yi awon gaba da wata jaririya yar watanni 3

Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa
Maryam da Maryam

Maryam Yahaya:

Budurwa yar shekara Ashirin da daya da ta yi zarra a sha’anin fina finan Hausa, an haifeta a unguwar Goron Dutse na jihar Kano, ta yi karatu a firamari na Yelwa, sa’annan ta yi sakandari a makarantar Barikin Bukabu. Maryam ta fara samun daukaka a fim din Mansoor.

Maryam Booth:

Hausawa na cewa barewa ba za ta yi gudu ba danta kuma ya yi rarrafe ba, hakan ne ya tabbata akan Maryam, wanda diya ce ga fitacciyar jarumar Kannywood, Zainab Booth, kuma an haifeta ne a shekarar 1993, inda ta fara fim tana shekara takwas, amma bata shahara ba sai a fim din Dijangala wanda ake yi shi a shekarar 2002.

Mai laya ya kiyayi mai zamani: Jaruman Kannywood 4 da tauraruwarsu ke haskawa
Miko da Umar

Umar M Sheriff:

Jama’a da dama sun fi sanin Umar da harkar waka, wanda lissafi ya tabbatar da yana da wakoki akalla guda dari biyar da suka shafi fannoni daban daban na rayuwar dan Adam, haifaffen Kaduna ne amma a iya cewa ya shiga Fim da kafar dama, kuma ya samu daukaka a Fim din Mansur. Haka zalika shima yana da fina finai da suka hada da Mahaifiyata, Nas, Jinin Jikina, da Ba zan barki ba.

Gazali Miko:

Dayake komai na Allah ne, daga haskaka daukar Gazali ya fara, amma a yanzu ya ciri tuta a shirin fina finan Hausa a sanadiyyar kyakkyawar alakarsa da Sarkin Kannywood, Ali Nuhu wanda ya sanya shi a cikin wani fim dinsa mai suna ‘Gamu nan dai’.

Daga cikin fina finan da Miko ya fito akwai Hadari, Ameerah, Zee Zee, Guguwar so, Makaryaci da Wata Dukiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng