Ambaliyar Katsina: Yadda ya ruwa ya yi awon gaba da wata jaririya yar watanni 3
A cigaba da bibiyan ambaliyan ruwa da ya faru a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina wanda ya faru a ranar Litinin din data gabata, BBC Hausa ta ruwaito daga cikin wadanda suka rasa ransu akwai wata yar jaririya da ruwan yayi awon gaba da ita.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani bawan Allah mai suna Attahiru ya shaida ma wakilinta cewa kimanin watanni uku da suka gabata ne Matarsa ta haifi diya mace, wanda itace yarsu ta farko, hakan yasa suka rada mata suna Fatima.
KU KARANTA: Wata budurwa mai Aljanu ta tashi ajin dalibai a jami’ar Usmanu Danfodiyo
Sai dai kash, abinka da ajali, sai ga wannan ambaliya, kuma ya tafi da jaririyar, bugu da kari mahaifinta Attahiru yace ko shi ko matarsa babu wani mai hoton diyartasu, sakamakon hoto daya kacal ya dauka da jaririyar, kuma ruwa ya tafi da wayar da aka dauki hoton.
Daga karshe Attahiru ya bayyana cewa ya zama wajibi ya gode ma Allah duk da ibtila’in da ya shafesu, kuma tunda Matarsa na raye, yana fatan Allah zai kara azurtasu da wani haihuwar anan gaba.
A wani labarin kuma wata Amarya da bata wuce kwanaki uku a gidan Angonta ba ta rasa ranta a cikin wannan ambaliya, inda da sai bayan kwanaki uku aka gani gawarta a can cikin kasar Nijar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng