Assha: 'Yan bindiga sun sake yin mummunan ta'addi a wata kauye a Zamfara

Assha: 'Yan bindiga sun sake yin mummunan ta'addi a wata kauye a Zamfara

Hukumar Yan sanda reshen jihar Zamfara ta tabbatar da harin da wasu 'yan bindiga suka kai a garuruwan Sikida da Gyaddu a karamar hukumar Maradi inda suka kashe mutane uku.

Sanarwan ta fito ne daga bakin Kakakin hukumar, Mohammad Shehu, yayin da yake yiwa manema labarai jawabi.

Ya kuma ce 'yan bindigan sun tsere kafin jami'an hadin gwiwa na Yan sanda sun isa inda harin ta faru bayan an sanar dasu.

Assha: 'Yan bindiga sun sake yin mummunan ta'addi a wata kauye a Zamfara
Assha: 'Yan bindiga sun sake yin mummunan ta'addi a wata kauye a Zamfara

DUBA WANNAN: Yadda wani magidanci ya bi matarsa gidan iyayenta ya kashe ta saboda tayi yaji

Kakakin yan sandan kuma yace jami'an hukumar sun dakile wata harin da yan baranda suka kai a kauyen Dangebe dake karamar hukumar Zurmi dake Zamfara.

"A yau 17 ga watan Yulin shekarar 2018 misalin karfe 8.30 na dare, wasu kumgiyar 'yan bindiga/barayin shanu sun ziyarci garin Dangebe da niyyar su saci shanu daga hannun mazauna kauyen.

"Jami'a na musamman sunyi tasan ma 'yan bindigan inda aka dauki lokaci ana musayar wuta wanda hakan ya sanya 'yan bindigan suka tsere suka koma cikin daji da raunukan bindiga," inji shi.

Kakakin hukumar yan sandan yace an kwato shanu 171 wanda yan bindigan su kayi niyyar sacewa.

"A halin yanzu, hukumar yan sanda ta baza jami'an ta don su bazama cikin dajin saboda a kamo 'yan bindigan da suka tsere," inji shi.

Ya kuma yi kira ga al'umma su cigaba da bawa hukumar hadin kai ta hanyar sanar da jami'an tsaron bayanai da zai taimaka musu wajen kare lafiya da dukiyoyin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164