Yadda daga addu'a wani dan tsibu ya zake wa wata daliba
- Hukumar Yan sanda ta kama wani dan tsibu mai shekaru 23 bisa zarginsa da yiwa wata yar shekaru 29 fyade
- Dan tsibun mai suna Mustapha Hammed, ya yiwa matar karyar cewa anyi masa wahayin cewa zata mutu
- Ya kuma shaidawa matar cewa za'a iya kawar ta mutuwar nata idan a kayi mata wankan tsarki kuma ta amince da hakan
Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta kama wani dan tsibu mai shekaru 23 mai suna Mustapha Hammed saboda zarginsa da yiwa wata dalibar Kwallejin Ilimin Fasaha dake Akoka Legas fyade.
Punch ta ruwaito cewa Hammed ya fadawa dalibar cewa ya gano cewa zata mutu cikin sa'o'i 24 muddin ba ta amince anyi mata wankan tsarki ba.
DUBA WANNAN: Rundunar Soji ta damke manyan dilolin kwaya a jihar Bauchi
Legit.ng ta tattaro cewa an tafi da dalibar unguwar Itowolo dake yankin Ikorodu dake Legas inda za'ayi mata wankan tsarkin.
A yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Litinin 16 ga watan Yuli, kwamishinan Yan sandan Legas, Edgal Imohimi yace: "Dan tsibun ya yaudari dalibar cewa ya gano zata mutu cikin sa'o'i 24. Ya kaita Ikorodu dake Legas don yi mata wankan tsarki amma yayi mata fyade duk da cewa yarinyar bata taba saduwa da na miji ba.
"Mahaifin yarinyar yace tun bayan afkuwalar lamarin, yarinyar ta fita hayyacin ta kuma tana cikin damuwa game da abinda dan tsibun ya aikata gareta."
Wanda ake tuhumar, dan asalin jihar Oyo, ya amsa cewa shi ne ya kawar wa yarinyar da budurcinta bayan ya sadu da ita a gidansa dake Ikorodu don yi mata wankan tsarki.
Kamar yadda kwamishina Yan sandan ya bayyana, a halin yanzu an tura binciken lamarin zuwa sashin kula da jinsi na hukumar don cigaba da bincike.
Ya kuma ce za'a gurfanar da wanda ake tuhuma gaban kotu bayan an kammala binciken.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng