Tunde Bakare yace ba wai ya je sanya baki ne kan batun Kemi Adeosun ba a wurin Buhari

Tunde Bakare yace ba wai ya je sanya baki ne kan batun Kemi Adeosun ba a wurin Buhari

- Fasto Tunde Bakare ya bayyana abinda ya kai shi fadar shugaban kasa dake Abuja a jiya

- Fasto Bakare ya karyata jita-jitar da ake yadawa da cewa ya tafi rokon alfarma ne dangane da badakalar kirkiri takardan shaidar kammala NYSC na Kemi Adeosun

- Yace ya tafi don mika godiyarsa ga shugaban kasar ne bisa gudunmawar da ya bashi lokacin jana'izar mahaifiyarsa

Shugaban cocin LatterRain Assembly, Fasto Tunke Bakare yace ganawar da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari a jiya bata da wani alaka da zargin da ake yiwa Ministan Kudi na kasa, Kemi Adeosun da laifin gabatar da takkatar NYSC ta bogi.

Vanguard ta ruwaito cewa Fasto Bakare yace ya ziyarci shugaban kasar ne kawai domin ya yi masa godiya bisa tawagar da ya aike wajen jana'izar mahaifiyar Fasto Bakare da akayi a kwanakin baya.

An bayyana abinda shugaba Buhari ya tattauna da Fasto Bakare a ganawarsu

An bayyana abinda shugaba Buhari ya tattauna da Fasto Bakare a ganawarsu

Kalaman Faston: "Labarin da ke yawo kafafen yadda labarai da dandalin sada zumunta tun jiya ba gaskiya bane. Ni da Ministan Kudi Kemi Adeosun mun ziyarci fadar shugaban kasar ne a lokuta mabanbanta.

"Mun hadu a cikin harabar Aso rock. Ta tafi ganawa da wani daban ne a fadar shugaban kasar yayin da ni kuma na gana da shugaba Muhammadu Buhari inda nayi masa godiya bisa yadda ya turo tawaga mai karfi zuwa jana'izar mahaifiyata. Wannan shine gaskiyar lamarin.

"Jita-jitar da ake ta yadda wa na cewa tare muka tafi zuwa ganin shugaban kasa ba gaskiya bane. Wannan kuskure ce. Zan so a wallafa labarin kamar yadda ta fito daga baki na."

Legit.ng kuma ta kawo muku cewa shugaban kwamitin shugaban kasa kan rashawa, Itse Sagay, ya yi kira ga hukumar NYSC ta bayyana gaskiyar lamarin abinda ya faru kan zargin takardan kammala NYSC ta bogi da ake zargin Kemi Adeosun ta aikatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel