An kama wani dattijo a Katsina dake yiwa barayin shanu safarar bindigogi

An kama wani dattijo a Katsina dake yiwa barayin shanu safarar bindigogi

- Yan sanda sun damke dalilin bindigogi dake sayar wa barayin shanu bindigogi a Katsina

- Kakain Yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, yace an kama wanda ake zargin ne a ranar Litin 9 ga watan Yuli a cikin dokan daji

- Isah yace wanda ake zargin yana taimakawa 'yan sanda wajen bincike a halin yanzu

Hukumar Yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da kama wani dalilin bindigogi mai shekaru 50 mai suna Safiyanu Amadu a jihar Katsina.

Punch ta ruwaito cewa Amadu wanda dan asalin kauyen Barbelu ne dake karamar hukumar Bakori ya dade yana sayarwa 'yan fashi da makami, barayin shanu da masu satar mutane da ke boye a dajin Rugu bindigogi.

An damke wani dalilan bingida mai shekaru 5 a jihar Katsina

An damke wani dalilan bingida mai shekaru 5 a jihar Katsina

DUBA WANNAN: Mutum uku ne ashe suka kashe diyar mataimakin gwamnan Ondo

Legit.ng ta tattaro cewa Kakakin hukumar Yan sanda jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da kama dilalin a ranar Litinin 9 ga watan Yulin 2018.

Lokacin da aka kama shi, an same shi da Kananan bindaga 'Pistol' guda biyu, da harsashi 7.62MM na bindiga kirar AK 47.

Kalaman Isha: "Bayan samun bayanan sirri da hukumar Yan sanda tayi, anyi nasarar damke wani gawurtaccen dalilin bindigogi wanda ya shahara wajen sayar wa 'yan fashi da makami da barayin shanu da masu satar mutane dake buya a dajin Rugu ta karamar hukumar Safana ta jihar Katsina makamai.

"Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda yace ya yi niyyar sayarwa wasu barayin shanu dake cikin dajin ne makaman. Yana kuma taimakawa yan sanda cigaba da gudanar da bincike."

Kazalika, rundunar ta kuma kama wasu gungun yan fashi da makami da garkuwa da mutane su tarra.

Sanarwan kamun ya fito ne daga bakin kakakin hukumar Yan sandan a hirar da ya yi da City News a Katsina, yace an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Faskari bayan wasu sun tseguntawa hukumar inda bata garin ke buya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel