Sai an kori bara-gulbi daga cikin jami'an soji sannan za a iya shawo kan kashe-kashe a Najeriya

Sai an kori bara-gulbi daga cikin jami'an soji sannan za a iya shawo kan kashe-kashe a Najeriya

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon (murabus) ya hori hukumar sojin Najeriya ta tabbatar cewa ta sallami dukkan bara-gulbin jami'anta da aka samu da hannu da aikata laifuka kuma a yi musu shari'a domin ta wanke kanta daga zargin da ake mata.

A wata sanarwa daya ya fitar da bakin mai magana da yawunsa, Alex rwang Pam, Janar Gowon ya yi wannan kirar ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga Ciyaman na kungiyar masu sarautun gargajiya na jihar Filato, Gbong Gwom Jos, Jacob Gyang Buba a fadarsa sakamakon kashe-kashen da akayi a jihar cikin kwanakin nan.

Gowon yayi kira ga hukumar sojin Najeriya sun fatataki balagulbi daga cikinsu
Gowon yayi kira ga hukumar sojin Najeriya sun fatataki balagulbi daga cikinsu

DUBA WANNAN: Mutum uku ne ashe suka kashe diyar mataimakin gwamnan Ondo

Tsohon shugaban kasar yace kashe-kashen da akayi rashin imani ne da tausayi, musamman idan akayi la'akari da cewa mutanen da aka kaiwa hare-haren basu aikata wani laifi ba. Yace hankalinsa ya tashi sosai bayan an nuna masa hotunan irin barnar da akayi lokacin yana Landan.

Bayan ya yi addua samun sauki ga wadanda ke jinya a asbiti tare da mika ta'aziyyarsa ga iyalan wanda suka rasa rayyukansu, Gowon yace bai taba ganin irin wannan kashe-kashen ba tun bayan yakin basasar da akayi a shekarar 1960.

A bangarensa, Gbong Gwom Jos ya mika godiyarsa bisa kulawa da Gowon keyi ga al'ummar jihar, ya kuma kara da cewa masu kashe-kashen suna da niyyar kwace wa mutanen sa kasarsu ne.

Basaraken ya roki Gowon ya taimaka ya saka baki a batun saboda gwamnatin tarayya ta taimakawa mutanen garin su samu su dawo gidajensu domin itace kadai abinda suka mallaka. A cewarsa, hakkin gwamnatocin ne su tabbatar cewa babu wanda ya kwace wa al'umma kadarorinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164