Mutum uku ne ashe suka kashe diyar mataimakin gwamnan Ondo

Mutum uku ne ashe suka kashe diyar mataimakin gwamnan Ondo

Alao Adeyemi, saurayin Khadijat Olubuyo, diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lasisi Olubuyo, yace bashi da hannu cikin kashe ta.

Mr Adeyemi ya yi wannan furucin ne yayin da manema labarai su kayi hira dashi hedkwatan Yan sanda dake Akure a ranar Laraba.

A cewarsa, wasu matasa biyu da diyar tsohon gwamnan ta tahoi dasu gidansa ne suka kashe ta.

A bangarensa, Kakakin hukumar Yan sandan jihar, Mr. Femi Joseph, yace sauran wadanda ake zargi guda biyun sun tsere bayan aikata mummunan aikin.

Yadda aka kashe diyar tsohon mataimakin gwamna a gidana - Adeyemi

Yadda aka kashe diyar tsohon mataimakin gwamna a gidana - Adeyemi

DUBA WANNAN: Bana nadamar tsigeni daga mukamina da aka yi

Mr. Adeyemi yace sunyi shekaru hudu suna soyaya amma sun rabu a shekarar 2015 sai dai sunyi sulhu bayan azumin wata Ramadana amma kawai yana taimaka mata wajen Project na kammala digirin ta ne.

Adeyemi ya ce, "Khadijat ta iso gidana a ranar Litinin inda ta fada masa cewa tana son ta sauki baki a gidana kuma na amince saboda wannan ba shine karo na farko da take aikata hakan ba.

"Daga baya sai ta shigo da maza biyu ni kuma na fice na basu wuri amma bayan mintuna 30 sai daya daga cikinsu ya kira ni, bayan na shigo sai naga daya daga cikinsu rike da bindiga shi kuma dayan ya shege mata wuya bayan ya yi mata zindir.

"Bayan ta mutu saboda mukurar da ya yi mata sai suka umurci ni in haka rami a dakina in rufe ta kuma su kayi barazanar harbi na idan nayi ihu ko na fada ma wani."

Kwanaki biyar bayan afkuwar lamarin sai na fadawa kani na abinda ya faru shi kuma ya sanar da mahaifinmu.

"Mahaifinmu ne ya sanar da 'yan sanda abinda ya faru sannan aka kama ni," inji Adeyemi.

Kakakin hukumar Yan sandan, Mr Adeyemi yace za'a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel