Tsiyar Nasarar: Sanata, dan majalisar wakilai da bulaliyar majalisa a jihar Fayose sun koma APC
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya rasa wasu kusoshi a jihar sa bayan sun tsallaka zuwa jam'iyyar APC ana saura kwana hudu zaben gwamnan jihar.
Daga cikin kusoshin da suka sulale daga PDP zuwa APC a yau akwai; Sanata Fatima Raji Rasaki, dan majalisar tarayya Olamide Oni da kuma bulaliyar majalisar jihar Ekiti, Sunday Akinniyi.
Sanata Rasaki na wakiltar yankin jihar Ekiti da ya mafi girma kuma daga yankin ne Fayemi ya dauko dan takarar mataimakinsa, Cif Bisi Egbeyemi.
Canjin shekar kusoshin na PDP wata manuniya ce cewar jam'iyyar ba zata kai ga nasara ba a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, mai zuwa.
DUBA WANNAN: Hotuna daga taron yiwa dan takara APC kamfen a zaben Ekiti da su Buhari, Osinbajo da jiga-jigan 'yan APC suka halarta
Da yake jawabi amadadin masu canja shekar, Sanata Rasaki, ta bayyana cewar sun fice daga PDP ne saboda karfa-karfa da Fayose ya yi masu wajen kakaba mataimakinsa a matsayin dan takarar gwamnan jihar.
Wasu masu nazarin siyasar yankin kudu maso yammacin Najeriya na 'yan kabilar Yoruba, sun bayyana cewar canjin shekar aikin jagoran jam'iyyar APC ne wato Bola Tinubu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng