Tabarbarewan Tsaro: Shugabanin kudu da yankin Arewa ta tsakiya sun gana da T.Y Danjuma
Wasu shugabanin kudu da yankin Arewa ta tsakiya sun gana da tsohon ministan tsaro na Najeriya, Theophilus Danjuma a kan tabarbarewan harkokin tsaro a wasu sassan kasar.
Shugabanin sunce Najeriya tana cikin halin tsaka mai wuya saboda hakan suka roki Mr Danjuma ya taimaka wajen ceto Najeriya daga halin da ta shiga.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, tawagar shugabanin karkashin jagorancin Edwin Clark sun nuna bacin ransu game da yadda ake gudanar da shugabancin kasar musamman harkar tsaro, sunyi gargadin cewa kasar na gab da rugujewa idan ba'a dauki mataki ba.
DUBA WANNAN: Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki
Shugaban Ohanaeze Ndigo, John Nwodo ya shaidawa Premium Times a hirar tarho cewa sun tuntubi Mr Danjuma ne saboda "shi dan siyasa ne wanda baya nuna bangaranci kuma ko banbanci a Najeriya."
"Mu shugabanin kudu da Arewa ta tsakiya mun gana da dattijon Najeriya T.Y Danjuma ne saboda mu lalubo hanyoyin da zamu ceto kasarmu daga rashin tsaro da tabarbarewar doka," inji shi.
Ya ce tawagar tasu zata ziyarci dukkan masu ruwa da tsaki da dattawa a Najeriya wanda suke ganin zasu iya kawo canji a Najeriya saboda a dawo da zaman lafiya da hadin kai a kasar.
"Dole a dena kashe-kashen da ake yi. Mene yasa sai bayan an gama kashe-kashe ne zaka ga Yan sanda da sojoji sun hallara? Hakan ya nuna akwai babbar matsala a kasa," inji shi.
Cikin wanda suka hallarci ganawar da T.Y. Danjuma sun hada da Chukwuemeka Ezeife, Ferdinand Agu, Ben Dike, Humphrey Orjiakor, C.R. Eherika, Idongesit Nkanga, Tony Nyiam da Godswill Igali.
Sauran sune Ayo Adebanjo, Dan Suleman, Olu Falae, Yinka Odumakin, Banjo Akintoye, Broderick Bozimo, Alfred Mulade, Tonye Douglas, Bitrus Dogu, Maryam Yunusa, Tanko Abdullahi da ma wasu saura.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng