Yanzu Yanzu: An ji karar bindiga yayin arangama tsakanin 'Yan sanda da Peace Corps a Abuja

Yanzu Yanzu: An ji karar bindiga yayin arangama tsakanin 'Yan sanda da Peace Corps a Abuja

A safiyar yau Talata 10 ga watan Yuli ne wasu jami'an 'Yan sanda da jami'an Peace Corps su kayi arangama a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Rikicin ya barke ne yayin da jami'an Peace Corp suka tattaki zuwa hedkwatan hukumar dake Abuja don murnar cika shekaru 20 da kafuwar hukumar ta Peace Corp.

Sai dai hedkwatan hukumar dama ya kasance a kule kuma yan sanda na gadinsa kusan na tsawaon shekara guda.

Yanzu Yanzu: An ji karar bindiga yayin arangama tsakanin 'Yan sanda da Peace Corps a Abuja
Yanzu Yanzu: An ji karar bindiga yayin arangama tsakanin 'Yan sanda da Peace Corps a Abuja

DUBA WANNAN: Hukumar soji ta saki kananan yara da Boko Haram ke amfani da su wajen yaki

Jami'an Peace Corp sun isa hedkwatan sanye da bakaken riguna dauke da rubuce-rubuce wanda ke bayyana rashin jin dadinsu da kin amincewa da kafa hukumar a Najeriya.

Shugaban hukumar, Dickson Akoh, yana gabatar da jawabinsa ga wanda suka hallarci taron kwatsam sai yan sanda iso wajen suna harbe-harbe tare da watsa barkonon tsohuwa don tarwartsa masu taron.

Ku biyo mu don samun karin bayani...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164