Da Azikiwe yana raye tabbas zai goyawa Buhari baya
Direkta Janar na muryar Najeriya (VON), Osita Okechukwu ya ce da tsohon shugaban kasar Najeriya na farko Dr. Nnamdi Azikiwe yana raye, da ya goyi bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Okechukwu yace hakan ne zai baiwa kabilar Igbo damar samun darewa shugaban Najeriya a shekarar 2023.
Ya kuma ce 95% na al'ummar Ibo da ke bukatar a yiwa kundin tsarin Najeriya garambawul suna basu son a raba Najeriya.
DUBA WANNAN: Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki
Okechukwu ya yi wannan jawabin ne a taron gwamnonin Kudu maso gabashin Najeriya inda suke bukatar a yiwa kudin tsarin Najeriya garambawul da akayi a ranar Lahadi da ta gabata a gidan gwamnati dake Enugu.
Ya kuma ce goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 shine hanya mafi inganci da tabbas da kabilar ibo zasu samu damar fitar da dan takarar shugabancin kasa a Najeriya.
Ya ce hakan zai kawo karshen koken wariya da kabilar Ibo suka dade suna yi na tsawon shekaru kuma zasu kafa kansu a wurare da dama a siyasar Najeriya.
A martaninsa ga kirar da shugaba Muhammadu Buhari ya yi ta bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a Owerri inda ya ce kabilar ibo zasu samu daman fitar da shugaban kasa ya rataya ne kan goyon bayan shugaba Buhari, Osita ya ce wannan kallubale ne ga mutanen yankin.
Ya yi kira ga masu jefa kuri'a daga yankin arewa da kudu su marawa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben na 2019 sannan daga baya sai yankin ta nemi fitar da dan takarar a 2023.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng