Bambarakwai: An kama ‘yan bijilanti 11 bisa zargin kisan ‘yan ta’adda 41 a Zamfara

Bambarakwai: An kama ‘yan bijilanti 11 bisa zargin kisan ‘yan ta’adda 41 a Zamfara

Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Zamfara ta tabbatar da kama ‘yan bijilanti da aka fi sani da “yansakai” 11 bisa zarginsu da kisan ‘yan ta’adda 41.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau Lahadi a Gusau.

An samu gawar wasu mutane 41, da ake zargin ‘yan ta’adda ne, a wani daji dake karamar hukumar Zurmi a satin day a gabata.

Bambarakwai: An kama ‘yan bijilanti 11 bisa zargin kisan ‘yan ta’adda 41 a Zamfara
Buhari da gwamnan jihar Zamfara yayin wata ziyara

Shehu ya bayyana cewar an kama mutanen 11 ne a jiya, Asabar, a maboyarsu daban-daban dake garin Kasuwan Daji a karamar hukumar Kaura-Namoda.

Ya kara da cewar ‘yan sanda na binciken a kan lamarin da kuma mutanen da aka kama kafin a gurfanar das u a gaban kotu.

DUBA WANNAN: Dogara ya bayyana abu daya tilo da zai iya kawo karshen rikicin jam’iyyar APC

Muna son yin amfani da wannan dama domin mika godiyar mu ga jama’a bisa samar da bayanai ga hukumar mu da suka kai ga kama mutanen.

“Muna kara kira gare su das u cigaba da bawa jami’anmu hadin kai domin cigaba da yaki da aiyukan ta’addanci a jihar Zamfara,” a cewar Shehu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng