Manomi ya datse hannun makiyayi saboda dabobinsa sun ci masa amfanin gona

Manomi ya datse hannun makiyayi saboda dabobinsa sun ci masa amfanin gona

A jiya Alhamis, ne wata kotun majistare dake Ilorin ta garkame wani manomi, Kabiru Garba, a gidan yari saboda tuhumarsa da akeyi da datse hannun wani makiyayi mai suna Mohammed Haliru.

Alkalin kotun, Kudirat Yahaya ta bayar da umurnin a kulle wanda ake tuhumar a gidan kurkuku na tarayya dake Oke-Kura, Ilorin kuma ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Yuli.

Manomi ya datse hannun makiyayi saboda dabobinsa sun ci masa amfanin gona
Manomi ya datse hannun makiyayi saboda dabobinsa sun ci masa amfanin gona

KU KARANTA: 'Yan sanda sun samu gawar 'yan ta'addan Zamfara 41 da aka kashe

Dan sanda mai gabatar da kara, Inspekta Mathew Olongbonsaye, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhumar mazaunin kauyen Kpada a karamar hukumar Patigi a jihar Kwara ya datse hannun Haliru ne saboda shanunsa sunyi kiwo a gonarsa.

Ya ce an gurfanar da Garba ne bisa laifin yiwa Haliru mummunar rauni wanda hakan ya sabawa sashi na 247 na dokar Penal Code.

Ologbonsaye yace an kama wanda ake tuhumar ne a ranar 10 ga watan Yuni bayan wani Wakili Abubakar dake rugar Fulani na Reshe-Kpada a Patigi ya kai kara ofishin yan sanda dake Patigi.

Abubakar ya yi ikirarin Haliru ya kaiwa dan uwansa hari ne da adda inji dan sandan mai shigar da kara.

Dan sanda mai shigar da karar kuma ya bukaci kotu ta cigaba da tsare wanda ake tuhumar a gidan yari har zuwa lokacin da za'a yanke hukunci a kan shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164