An kashe sojoji 2, sannan an jiwa kwamanda da wasu sojoji 5 ciwo
Helkwatar tsaro ta kasa dake babban birnin tarayya, tace wasu makiyaya dauke da makamai sun kaiwa rundunar sojoji mai taken 'Operation Whirl Stroke' a karamar hukumar Keana dake jihar Nasarawa, inda suka kashe sojoji biyu sannan suka jiwa sojoji biyar ciwo ciki kuwa hadda Kwamandan su guda daya a ciki
Helkwatar tsaro ta kasa dake babban birnin tarayya, tace wasu makiyaya dauke da makamai sun kaiwa rundunar sojoji mai taken 'Operation Whirl Stroke' a karamar hukumar Keana dake jihar Nasarawa, inda suka kashe sojoji biyu sannan suka jiwa sojoji biyar ciwo ciki kuwa hadda Kwamandan su guda daya a ciki.
DUBA WANNAN: Ya kone 'yar yayanshi saboda tana shiga gidan makota
A ranar Larabar nan ne helkwatar tsaron tace rundunar sojojin sun kama mutane 21 daga cikin masu tada zaune tsaye a jihar Nasarawa da kuma mutane 13 a jihar Benue.
Rundunar tace makiyayan sun kawo harin ne a ranar Talatar nan, amma duk da haka rundunar ta samu nasarar kwace makamai ciki kuwa hadda bindigogi guda 3 da kuma harsashi guda 800.
An kafa rundunar sojoji ta 'Operation Whirl Stroke' a ranar 8 ga watan Yunin nan a karkashin hukumar tsaro ta kasar nan domin kawo zaman lafiya a jihohin Benue, Nasarawa, Taraba, da kuma jihar Zamfara, wadanda a yanzu haka suke cikin matsalolin rashin tsaro na makiyaya.
"Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Muhammad Hussein, ya zargi hukumar soji da kashe Fulani 6 da kuma daruruwan shanaye, a wata jarida da aka fitar ranar 28 ga watan Yuni. Wannan magana ba haka take ba, kuma labarin bashi da tushe.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng