'Yan sanda sun samu gawar 'yan ta'addan Zamfara 41 da aka kashe
Hukumar Yan sandan Najeriya ta sanar da cewa jami'anta sun samu gawarwakin mutane 41 wanda aka yiwa yankan rago a wani daji da 'yan ta'adda da sauran miyagun mutane suke buya a Zamfara.
Kamar yadda kwamishinan yan sanda Kenneth Ebrimson ya fadi a ranar Talata, an gano gawawaki 18 a cikin rafi a ranar Lahadi yayin da sauran 23 kuma an gano su ne a wani daji dake Zurmi a jihar Zamfara.
DUBA WANNAN: Shugaban INEC zai bayyana a gaban kotun Abuja bayan PDP ta shigar da shi kara
Yan sandan kuma sun damke wasu mutane hudu da ake zargin yan ta'adda bayan an same su dauke da bindigogi da adduna kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Ya ce ana kyautata zaton wadanda aka kama mambobin kungiyar yan banga ne da suke ta kashe mutane babu-gaira-babu dalili da satar shanu da garkuwa da mutane a sassan jihar.
Sai dai mazauna kauyen basu iya gane gawarwakin mutanen da aka tsinta ba wanda hakan ke nuna cewa mutanen ba mazauna yankin bane.
'Yan bindigan sun kwashe shekaru suna musgunawa mazauna kauyukan Zamfara inda suke sace musu shanu da kona musu gidaje da kuma sace mutane don a biya su kudin fansa.
Bayan sun aikata barnarsu, yan bindigan sukan shige dajin Raggu don buya. Dajin yana da iyaka da jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina.
A watan Afrilun wannan shekarar ne gwamnatin tarayya da aike da dakarun soji jihar Zamfara don kawo karshen kashe-kashen da akeyi tsakanin yan ta'addan da yan banga a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng