2019: Wasu cikas da tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso zai iya gamuwa da su
Bisa dukkan alamu tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yana neman yayi takarar Shugaban Kasa a zaben 2019. Sai dai hakan na iya masa wuya saboda wasu dalilai da masana harkar siyasa su ka gindaya.
A Jihar Kano ma dai sai Sanatan yayi da gaske zai iya samun tikitin Jam’iyyar APC na tsayawa takarar kujerar sa ta Sanata. Tsohon Gwamnan ya samu sabani da Mai Girma Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ya ke tare da Shugaba Buhari.
KU KARANTA: Kishin-kishin: Za ayi wa Buhari taron dangi a zaben 2019
Ga kadan daga cikin matsalolin da Sanatan zai iya samu a tafiyar siyasar sa:
1. Tikitin APC
Zai yi matukar wahala dai Jam’iyyar APC ta ba Sanata Rabiu Kwankwaso tikitin takara a zabe mai zuwa ganin cewa Shugaba Buhari ya nuna cewa zai zarce. Kusan ma dai makomar Kwankwaso a Jami’iyyar na yawo ne a iska.
2. PDP
Sanatan na Kano yana cikin ‘Yan nPDP wadanda su ke kukan ba ayi masu adalci a Jam’iyyar APC mai mulki. Sai dai Shugaban kasa Buhari ma yayi banza da su ya nuna cewa ba zai gana da su har ma ta kai ya ji matsalolin su ba. Hakan dai na nufin cewa ‘Yan nPDP din su na fuskantar barazana.
3. Sabuwar Jam’iyya
Akwai rade-radin cewa Sanatan yana neman Hukumar INEC ta kasa tayi masa rajistar Kungiyar Kwankwasiyya a matsayin Jam’iyyar takara. Sai dai Kwankwaso na iya gamuwa da babbar matsala ko da an yi wa Jam’iyyar rajista musamman wajen kudi da kuma karbuwa a kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng