2019: Jerin tsofin janar-janar na soji dake kulle-kullen kayar da Buhari zabe

2019: Jerin tsofin janar-janar na soji dake kulle-kullen kayar da Buhari zabe

Bincike ya tabbatar da cewar wasu daga cikin manyan tsofin janar-janar na hukumar sojin Najeriya sun hada kai domin tabbatar da cewar shugaba Buhari bai sake cin zaben shugabancin kasa ba a zaben shekarar 2019 mai zuwa, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Kazalika, binciken jaridar ya gano cewar, tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji da farar hula, Janar Olusegun Obasanjo (mai ritaya) ne ke jagorancin tsofin sojojin.

Tsofin janar-janar din na burin ganin Buhari bai cigaba da zama a fadar gwamnatin Najeriya ba saboda hankalinsu bai kwanta da irin manufofi da tsare-tsaren gwamnatinsa ba, hakan ya saka su hada wata tafiya domin yin makarkashiyar da zata kai ga kayar da Buhari a 2019.

2019: Jerin tsofin janar-janar na soji dake kulle-kullen kayar da Buhari zabe
Shugaba Buhari

Wasu daga cikin fitattun tsofin janar-janar din dake kan sahun gaba wajen ganin Buhari bai sake samun dammar komawa kan karagar mulki ba akwai; Laftanal Janar Theophilus Danjuma, tsofin shugaban kasa a mulkin soji; Janar Ibrahin Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar, Janar Zamani Lekwot da Janar Joshua Dogonyaro da wasu da dama.

DUBA WANNAN: Tuna baya: Takaitaccen tarihin sadauki, Hassan Sarkin Dogarai

Duk da ko a tsakaninsu ba wata jituwa suke yi ba, amma a wannan karon bukatar kansu ta hada su wuri guda domin tsira tare. Kazalika dalilan da ya saka su adawa da shugabancin Buhari sun banbanta.

Wata majiya ta shaidawa The Nation cewar, Obasanjo ne ke jagorantar tafiyar. Watakila saboda gogewar sa da kuma yara da suke da su a siyasance

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng