Gobarar tankar dakon mai a Legas na daga cikin manyan da suka samu Najeriya - Buhari

Gobarar tankar dakon mai a Legas na daga cikin manyan da suka samu Najeriya - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana iftila’in gobarar tankar dakon man fetur da ya faru a Legas a mastayin daya daga cikin manyan annoba da suka faru a Najeriya a baya-bayan nan.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya raba ga manema labarai a Abuja.

Buhari ya bayyana cewar lamarin ya matukar girgiza shi da nuna alhininsa bisa asarar rayuka da dukiya da gobarar ta haifar.

Gobarar tankar dakon mai a Legas na daga cikin manyan da suka samu Najeriya - Buhari
Shugab Buhari

Da yammacin yau Alhamis ne wata babbar motar tanka ta kama da wuta a gadar Otedola dake wajen jihar Lagas, a kan babbar hanyar zuwa Ibadan.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya amince da kashe biliyan N10bn domin ragewa mutanen Filato da rikici ya shafa radadi

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) da hukumar kashe gobara ta jihar sun gaggauta zuwa wurin da abin ya afku. Kazalika rundunar ‘yan sanda ta ko-ta-kwana (RRS) ta ce ta tura jami’anta domin shawo kan lamarin. Saidai karfin wutar ya yiwa gaske saboda kasancewar motar na dauke ne da man fetur, sannan motocin dake kusa da wurin suma duk sun kama da wuta.

A cewar shaidu da abun ya afku a idanunsu, sunce wutar ta lashe sama da motoci 20 da kuma wasu mutane da ba’a san adadinsu ba akan gadar ta Otedola dake kan babban titin Legas zuwa Ibadan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng