Nigerian news All categories All tags
An garkame kasuwar yan Nama sanadiyyar rikici da ya kaure tsakanin Yansanda da Mahauta

An garkame kasuwar yan Nama sanadiyyar rikici da ya kaure tsakanin Yansanda da Mahauta

Gwamnatin jihar Oyo ta sanar da garkame kasuwar yan Nama dake Bodija, cikin garin Ibadan, sakamakon tumutsitsi da aka samu biyo bayan fada da ya kaure a tsakanin Mahauta da jami’an Yansanda, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnatin jihar ta sanar da haka ne ta shafinta na Twitter, inda tace ta dauki wannan mataki ne sakamakon karar harbe harbe da aka jiyo daga cikin kasuwar, don haka aka rufe kasuwar don gudun asarar rayuka da dukiya.

KU KARANTA: Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe

Shi ma shugaban hukumar mulki na Aare Laatosa na jihar, Adekunle Oladeji ya bayyana cewa wannan mataki na rufe kasuwar ya zama wajibi don gudun yaduwar rikicin zuwa wasu sassan kasuwar da sassan jihar ma gaba daya.

An garkame kasuwar yan Nama sanadiyyar rikici da ya kaure tsakanin Yansanda da Mahauta

Mahauta

Wannan rikici ya samo asali ne sakamakon umarnin da Gwamnatin jihar ta bayar ga mahauta da su tashi daga kasuwar Bodija su koma sabuwar kasuwar da gwamnatin jihar ta tanadar musu, sai dai mahautan sun ce ba zata sabu ba, don kuwa sabuwar kasuwar ta yi bayan gari dayawa.

Ko a ranar Talatar da gabata, sai da mahautan suka gudanar da zanga zanga zuwa sakatariyar garin Ibadan, inda suka nuna bacin ransu game da aikin rusau da gwamnatin ta kaddamar da wani sashi na kasuwar tasu.

Da wannan ne wasu daga cikin mahautan suka fara zargin wasu daga cikin shuwagabanninsu kungiyarsu da cewa suna amsan kudi daga gwamnati a matsayin toshiyar baki don neman bayansu ga tarewa a sabuwar kasuwar.

Dayake jawabi, Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace rundunar za ta fitar da bayani game da rikicin nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel