Ana wata ga wata: An kashe mutane 300 a wani sabon rikicin kabilanci a kudancin Najeriya

Ana wata ga wata: An kashe mutane 300 a wani sabon rikicin kabilanci a kudancin Najeriya

Wani rahoto da shafin jaridar BBC Hausa ta fitar dazun nan ya bayyana cewar fiye da mutane 300 ne aka kashe yayin da wasu da yawa suka raunata, wasu kuma suka salwanta a wani sabon rikicin kabilanci da ya barke tsakanin kabilun Ndi a jihar Ebonyi da Ukelle a jihar croos Rivers.

Kabilun biyu na rikici ne a kan filayen nomad a suka yi iyaka da juna, kuma kowannen su ke ikirarin shine ya mallaka.

Lokacin da sashen BBC na harshen Igbo ya ziyarci yankin da kabilar Ndi ke zaune a garin Ndi ta karamar hukumar Izzi, ta iske garin ya zama kango, ba kowa a gidaje, kasuwa, makarantu da wuraren ibada, saboda mutane sun kauracewa gidajen su.

Ana wata ga wata: An kashe mutane 300 a wani sabon rikicin kabilanci a kudancin Najeriya
Mutane sun gudu daga gidajen su

Sarkin garin Ndi ya shaidawa wakilin BBC cewar rikicin ya samo asaline bayan kabilun biyu sun fara ikirarin mallakar wani filin noma da ya ratsa ta cikin karamar hukumar ta Izzi. Rikici tsakanin kabilun biyu ya fara ne tun shekarar 2005.

Filin da ake rikicin a kan sa na da girma sosai da kuma wadatar koramun ruwa, kuma ya ratsa ta yankin garuruwan kabilun biyu dake zaune a jihohi daban-daban.

DUBA WANNAN: An kama masu garkuwa da mutane 12 a Sokoto

Wasu matasan kabilar Ndi da BBC ta tattauna da su, sun ci al-washin daukar fansar kisan ‘yan uwan su da suke zargin Ukelle ne suka kashe su.

Ko a jiya saida shugaba Buhari ya ziyarci jihar Filato bayan barkewar wani rikici tsakanin makiyaya da mazauna wasu kauyuka a karamar hukmar Barkin Ladi ya yi sanadiyyar rasa rayuka fiye da 200.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng