Rashin adalci ne a ce na yi shiru kan Kashe-Kashen Makiyaya - Buhari

Rashin adalci ne a ce na yi shiru kan Kashe-Kashen Makiyaya - Buhari

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kalubalanci masu zargin sa da cewar ya sanya idanu kurum kan kashe-kashen da makiyaya ke faman aiwatar wa cikin wasu sassa na kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana cewa masu gudanar da wannan zargi da tuhuma a kansa ba su aikata daidai tare da rashin adalci a gare sa.

Cikin jawaban kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki a birnin Jos na jihar Filato dangane da harin da ya afku cikin jihar a kwana-kwanan nan da ya salwantar da rayukan mutane da dama.

Shugaba Buhari yake cewa, watakila wasu al'ummar kasar nan na zargin sa da nuna halin ko in kula dangane da rikicin makiyaya sakamakon kamanceceniya da yake da ita irin tasu.

Rashin adalci ne a ce na yi shiru kan Kashe-Kashen Makiyaya - Buhari

Rashin adalci ne a ce na yi shiru kan Kashe-Kashen Makiyaya - Buhari

Ya nemi al'umman Najeriya akan kauracewa batutuwa da furuci waɗanda ka iya janyo barazana ga zaman lafiya da haddasa tashin-tashina a kasar nan.

Buhari, wanda ya halarci taron tare da gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da kuma takwarorin sa na jihar Kebbi na Neja, sun jajantawa 'yan uwa da al'ummar jihar dangane da ibtila'in da ya afka masa.

DUBA WANNAN: Ma'aikatu 50 na Gwamnatin Tarayya da babu Jagorori

Legit.ng ta fahimci cewa, sauran 'yan tawagar shugaban kasar sun hadar da; Ministan tsaro Mansur Dan-Ali, Ministan harkokin cikin gida Abdurrahman Danbazau da kuma Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammad.

Tawagar ta shugaba Buhar ta kuma hadar da; Shugaban hafsin sojin sama na kasa, Air Vice Marshall Sadique Abubakar da kuma sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim K. Idris.

Sauran jiga-jigan masu ruwa da tsaki da suka halarci taron ganawa da shugaba Buhari sun hadar da; Ma'aikatan Majalisun dokoki na jiha da na tarayya, Sarakunan Gargajiya da kuma shugabannin kungiyar Kirista ta Najeriya watau CAN da kungiyar Jama'atu Nasril Islam.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel