Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa

Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, John Obi Mikel yace ya kamata ace an baiwa 'yan kwallon Najeriya damar daukan Penalty wanda dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Argentina yayi

Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa
Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, John Obi Mikel yace ya kamata ace an baiwa 'yan kwallon Najeriya damar daukan Penalty wanda dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Argentina yayi.

Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yace baiga dalilin da ya hana a ba Najeriya damar penalty ba bayan Marcos Rojo ya taba kwallon da hannun shi kuma kowa ya gani.

DUBA WANNAN: Duba kasar da mata suka fi shiga hatsari a duniya

Argentina taci wasan, wanda zai bata damar kaiwa ga zango na gaba, inda zata fuskanci kasar Faransa.

Kaftin din Super Eagles, John Obi yace yakamata rafalin da ya shugabanci wasan tsakanin Najeriya da Argentina, Cuneyt Cakir, ya basu damar penalty.

Najeriya dai ta fita daga gasar kwallon kafa ta duniya na shekarar 2018 bayan da kasar Argentina ta lashe wasan jiya da ci2 da 1.

A lokacin da ake kunnen doki tsakanin Najeriya da Argentina, kwallon ta bigi hannun Marcos Rojo, dalilin da yasa a baiwa Najeriya damar daukan penalty din kenan, inda shi kuma rafalin yace a cigaba da wasa, wanda ya kawo cece-ku-ce daga yan wasan Najeriya.

John Obi Mikel yace rafalin ya bayyana mishi dalilin hanasu Penalty, inda yace "Idan ka kalli wasan Portugal jiya, wannan bai yi ko kusa da wancan ba. Wannan yafi wancan muni. Mun kuma gani.

Da Mikel ya tambaye shi mai ya hana a basu penalty din? Sai rafalin yace shima bai sani ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng