Da dumin sa: Shugaba Buhari ya bude wani katafaren asibiti da rukunin gidaje 100 na sojin sama a Calabar
A yau, Talata, ne shugaba Buhari ya wuce garin Calabar, babban birini jihar Cross River, inda ya bude wani katafaren asibiti da rukunin gidaje 100 na sojin sama. Rahotanni sun bayyana cewar kafin wucewar sa zuwa garin na Calabar, shugaba Buhari ya tsaya a jihar Filato inda ya jajantawa jama'a abinda ya faru na asarar rayuka da dukiya sakamakon rikicin da ya barke ranar Asabar.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a kasha-kashen jihar Filato, ya fadi abinda suke son cimma
Shugaba Buhari ya samu rakiyar wasu manyan jami'an gwamnatin sa da suka hada da ministan tsaro, Mansur Dan-Ali.
Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, da shugaban sojin sama, Siddique Abubakar na daga cikin jama'ar da suka tarbi shugaba Buhari da tawagar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng