Ba mu canja salon taken jam'iyyar mu ba - APC
Jam'iyya mai mulki ta APC ta ce karyata labarin da ke yawo a wasu kafafen yadda labarai na cewa ta canja salon taken ta daga "canji" zuwa "cigaba" kamar yadda wasu jam'iyyun siyasa biyu su kayi ikirarin cewa APC ta yi.
Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta zargi APC da yin amfani da taken ta na "cigaba".
Sakataren SDP na kasa, Shehu Gabam ne ya yi wannan zargin a wata jawabin manema labarai da ya kira a Abuja inda ya ce bincike n da suka gudanar ya nuna cewa jam'iyyarsu ce kadai tayi rajista da taken "cigaba".
Ya ce hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasa su bayar da taken jam'iyyarsu yayin da suke rajistan jam'iyyun.
KU KARANTA: Zan kawo karshen kashe-kashe idan aka zabe ni shugaban kasa - Makarfi
Mr. Gabam ya yi kira ga APC ta dena rudar da masu kada kuri'a musamman a yanzu da ake fuskantar babban zaben 2019.
"Doki mai gudu wanda shine alamar SDP yana nufin Cigaba. Alamar tsintsiya ba ta nufin cigaba," inji shi.
Ya kara da cewa tuni SDP ta shigar da APC kara a wajen hukumar INEC.
PDP ta ce shirin da APC ta yi na canjin taken ta 'tsabar rainin wayyo ne da yaudara ga yan Najeriya daga jam'iyyar da ba ta tabuka komai ba sai dai yunwa da wahalhalu da zubda jinin a kasar."
Sai dai Sakataren yadda labarai na APC, Mallam Ahmed Bolaji ya shaidaw Premium Times cewa APC ba ta canja taken ta ba.
Ya ce dole sai APC ta yi gyara a kundin tsarin jam'iyyar idan har tana son canja taken ta saboda taken jam'iyya yana daga cikin abubuwan da aka bayar wajen yin rajista.
Kawai don an ce APC kuma mutane sun amsa da "cigaba" ko makamancin haka baya nufin an canja taken jam'iyyar.
"Ba zai yiwu a canja taken jam'iyya da baki ba, dole sai anyi gyara a kundin tsarin jam'iyya. PDP da SDP kawai sun jahilci lamarin ne," inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng