Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya sa labule da Atiku Abubakar

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya sa labule da Atiku Abubakar

- Sanata Kwankwaso yayi watsi da babban taron APC da aka yi jiya

- An ga Babban ‘Dan siysar Arewan ya sa labule da Atiku cikin dare

- Kusan dai Atiku da Kwankwaso na neman takarar Shugaban Kasa

‘Daya daga cikin manyan ‘Yan Jam’iyyar APC tsohon Gwamna kuma Sanata na Kano watau Rabiu Musa Kwankwaso yayi watsi da babban taron Jam’iyyar APC na kasa da aka yi jiya Asabar.

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya sa labule da Atiku Abubakar
Sanatan Kano Kwankwaso tare da Atiku Abubakar a Abuja

Ba a ga duriyar Sanatan na Kano ta tsakiya Rabiu Kwankwaso a wajen gangamin APC da aka yi a babban Birnin Tarayya Abuja ba sai dai aka gan shi a gidan tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar inda su ka sa labule.

Masana harkar siyasar kasar dai sun ce babu mamaki shirin zaben 2019 ne ta sa tsohon Gwamnan wanda ke niyyar takarar Shugaban Kasa ya gana da Atiku Abubakar wanda tun a bara shi ya bar Jam’iyyar APC mai mulki ya koma PDP.

KU KARANTA: Inyamuran Najeriya za su goyi bayan Shugaba Buhari

Shugaban tafiyar Kwankwasiyyan ya shiga gidan Atiku Abubakar da ke Birnin Tarayya Abuja ne cikin dare da kimanin karfe 8:30. Ganawar ta su da babu wanda ya san abin da aka tattauna ta ci kusan mintuna 45 kamar yadda mu ka ji labari.

Wasu na cewa dai Sanatan na APC ya kai wa Atiku ziyarar Sallah ne ko da dai ba a taba jin tsohon Gwamnan ya kai wa Atiku wata ziyara ba. Dama dai Kwankwaso da wasu tsofaffin ‘Yan PDP da ke APC dai su na barazanar ficewa daga APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel