Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

Karshen duniya: An kama shi turmi da tabarya da matar mahaifin sa

An kama wani matashi Bubbingeon Museika Ndaba mai shekaru 25 yana tara wa da matar mahaifinsa a daji.

Wannan lamarin ya faru ne a kauyen Mudzami da ke Huchu a Gokwe ta kasar Zimbabwe, hakan yasa Sarkin Nemangwe wanda kauyen ke karkashin mulkinsa ya bayar da umurnin gudanar da bincike kamar yadda Bulawayo24 ta ruwaito.

Rahotanni sunce matar mahaifin Bubbingeon Museika Ndaba, Naume Langson ne ta yi masa dabara har ya fara kwanciya da ita saboda a cewarta mahaifinsa mai shekaru 67 baya iya gamsar da ita.

Asirinsu ya tonu ne bayan wani dan uwansu mai suna Bongani Ncube ta gama su turmi da tabarya a kusa da rafi.

KU KARANTA: Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

An kuma ce kafin a gano abinda suke aikatawa, an sha ganinsu suna zuwa dajin tare kuma ana kyautata zaton tun a lokacin suke aikata barnar tasu.

Bayan Ncube ta kama su, ya garzaya gidan inda ta sanar da mahaifin Museika Ndaba mai suna Isaac wanda shi kuma ya kai maganar wajen mai unguwa.

Museika Ndaba ya ce ya fara tarawa da matar mahaifinsa ne wata rana da ta shigo dakinsa ta iske shi zigidir yana barci saboda zafi, daga nan ne wai ta janyo hankalinsa har ta kai ga sun kwanta tare.

Ya ce ya yi kokarin ture ta daga jikinsa lokacin da ya farka daga barci amma hakan bai yiwu ba.

"Abinda na yi ba kuskure bane laifin da nayi kawai shine nayi da dan miji na saboda a gaskiya mijina baya gamsar da ni. Matsuwa ce ta janyo na aikata hakan da dansa kuma na roki mijina gafara kuma ya yafe min," inji Langson.

Cif Nemange wanda aka kaiwa kara ya ce wannan abin kunya ce matuka hakan yasa ya yanke hukuncin cinsu tara da shanu daya ko wannensu. Ya kuma kara da cewa Museika Ndaba ya kara wa mahaifinsa wani shanun saboda irin cin amanar da ya yi masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164