Hadamarku ta yi kamari - Shugaba Buhari ya fadawa 'yan majalisa

Hadamarku ta yi kamari - Shugaba Buhari ya fadawa 'yan majalisa

Har yanzu dai ana cigaba da musayar maganganu tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar Najeriya inda fadar shugaban kasar ta zargi 'yan majalisar tarayyar da hadama.

A baya, majalisar ta kare canje-canjen da tayi a kundin kasafin kudin na shekarar 2018 bayan shugaba Buhari ya nuna rashin gamsuwarsa kan ayyukan da suka kara.

Sai dai a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, fadar shugaban kasar ta ce bayan majalisar sun kara farashin danyen man fetir don su kadai su amfana, sun kuma rage kudaden da aka ware za'ayi wa talakawa ayyuka.

Zalamarku tayi yawa, Shugaba Buhari ya gaya wa 'yan majalisa
Zalamarku tayi yawa, Shugaba Buhari ya gaya wa 'yan majalisa

KU KARANTA: Kabilar Ibo a sun yunkuro kan batun kama Sanatansu da DSS tayi

"Fadar shugaban kasa tayi mamakin yadda majalisar ta rage kudaden manyan ayyuka duk da cewa ta kara wa kanta N170 biliyan don ayyukan mazabu baya ga N100 miliyan da aka riga aka ware musu na ayyukan. Wai har nawa suke bukata ne?" inji Adesina.

Sai dai su kuma a bangarensu, majalisar ta fadawa fadar shugaban kasa cewa tana gudanar da ayyukanta ne kamar yadda doka ta tanada kuma ba ita ba wata ma'aikata bane karkashin fadan shugaban kasar.

A martaninsa ga shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Dino Melaye ya ce babu wanda ya tilastawa shugaban kasa rattaba hannu a kan kasafin kudin muddin yana ganin akwai wuraren da bai gamsu da su ba.

Abinda ya dace ya yi kawai shine ya mayar wa majalisar kasafin kudin tare da abubuwan da bai gamsu da su ba a rubucce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel