Na fi ka rashin mutunci bana tsoran kowa sai Allah- Umma Shehu ga wani jigo na Kannywood

Na fi ka rashin mutunci bana tsoran kowa sai Allah- Umma Shehu ga wani jigo na Kannywood

Shahararriyar jarumar nan ta dandalin Kannywood, da tauraruwarta ke kan haskawa, Umma Shehu, ta shirya saka kafar wando daya da mai yi mata bita da kulli a masana'antar fim.

Ko da yake jarumar bata bayyana sunan wanda take caccaka ba, jarumar ta bayyana cewa baza ta damu ba idan har aka kore ta daga masana’antar.

A sakon da ta wallafa a shafin ta na kafar sada zumunta, Umma bata boye irin rashin mutunci da zata iya yi ga duk mutumin da ya tokale ta ba.

Na fi ka rashin mutunci bana tsoran kowa sai Allah- Umma Shehu ga wani jigo na Kannywood
Na fi ka rashin mutunci bana tsoran kowa sai Allah- Umma Shehu ga wani jigo na Kannywood

Tana mai cewa "Na fika rashin mutunci kuma ni da kake kallo bana tsoron kowa sai Allah".

Ga cikakken sakon da ta fitar kamar haka;

"Babu abunda ya dame ni da kai idan ka ga dama kasa a kore ni a kannywood dan nasan bakai ne me bada daukaka ba Allah ne dan haka wallahi na fi ka rashin mutunci ni da kake kallona ba na tsoran kowa sai Allah ni ummah Shehu nafi karfin na baka hakuri ba tare da na maka laifi ba dan kasa anyi casting dina sai me ka manta da Allah shine meyi kafin kaima kanka ai am maka dan haka ba cire ni ya kamata ayi ba korana ya kamata kayi nonsense ni ba zansa hoto ina fadanci ba don babu abunda nake nema agun kowa sai gun Allah kaje ka tambayi waye ummah shehu za’a gaya maka irin rashin mutuncin da zanyi kuma idan ka tashi tambaya kazo unguwarmu ka tambaya anan ne zaka ji ainihin halin ummah babu wanda ya isah naime fadanci idan ina sonka Ina sonka idan bana sonka bana sonka ni haka nake dan haka to hell with you".

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani na shirin isowa Lagas

Idan ba'a manta ba a kwanakin baya, Ummah Shehu, ta jawo tsegumi a kafafen sada zumunta bisa ga tambayoyi da mai gabatar da shiri yayi mata hirar ta da telebijin na Arewa24 a cikin wani shiri na musamman.

Bayan hirar dai jarumar ta fito fili ta bayyana cewa bata ji haushin abun da ya faru tsakaninta da mai gabatarwa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng