Sharri ake masa, Buhari bashi da hannu cikin kashe-kashen Benue - Matasan Benue
- Matasan Jihar Benue sunyi alkawarin bawa shugaba Muhammadu Buhari goyon baya
- Matasan sun karyata jita-jitan da ake yadawa da cewa shugaban kasan na da hannu cikin kashe-kashen da akeyi a Benue
- Sun kuma yabawa shugaban hafsin sojojin saman Najeriya bisa kokarin da ya keyi wajen kawo karshen kashe-kashe a Jihar
Matasan Jihar Benue sun wanke shugaba Muhammadu Buhari daga dukkan zargin da akeyi na alakanta shi da kashe-kashen da akeyi a Jihar.
Kungiyar matasan Benue BYF ta ce zargin da ake yiwa shugaba Muhammadu Buhari na daukan nauyin kashe-kashen da akeyi a Benue kawai sharri ne ake yi masa saboda dama wasu basu kaunarsa tun farko.
BYF kuma ta yi alkawarin bayar da goyon bayan 100% a kan yunkurin sa na kawo karshen kashe-kashe da ayyukan ta'addanci da ke yaduwa a Jihar ta Benuwe.
KU KARANTA: Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara
A yayin da suka yabawa da kokarin da sojojin Najeriya keyi a Benue da wasu jihohin Najeriya, kungiyar ta bukaci sojojin su kara zage damtse wajen fatatakar miyagu da bata gari a jihar.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shuganan kungiyar, Terrence Kuanum, ya ce kungiyar ta yabawa shugaban hafsin sojin kasar Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai bisa irin jagorancin da yake bawa sojin Najeriya da nasarorin da ya ke samu.
Kuanum ya ce: "Muna goyon bayan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a yunkurinta na kawar da ta'addanci kuma muna yabawa irin nasarorin da aka samu musamman a jihar Benue.
Munyi murna kan yadda aka gano wanda ya kashe hadimin gwamna Ortom wanda abu ne da ya tayar mana da hankali a jihar tare da tarwatsa kungiyoyin yan fashi da makami da garkuwa da mutane a jihar.
Za mu cigaba da goyon bayan dukkan yunkurin samar da zaman lafiya a kasa musamman a Benue. Munyi imanin cewa atisayen da sojin Najeriya ke yi zai kawo zaman lafiya mai dorewa a Benue," inji Kuanum.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng